9 Disamba 2017 - 15:34
ANYI MUZAHARAN ALLAH WADAI  GAME DA YUNKURIN MAI DA HELKWATAR ISRA'ILA ZUWA BIRNIN QUDUS A NIJERIYA

A jiya Juma'a ne, Yan Shi'a mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky a Nijeriya suka yi muzahara da gangami domin nuna goyon baya ga Palasdinawa da kuma Allah wadai da yunkurin haramtacciyar kasar Isra'ila na mai da helkwatar kasar zuwa birnin Qudus. Anyi wa'yannan muzaharorin a garuruwan Kano, Gombe da sauran wurare a fadin tarayyan Nijeriya. In ba a manta ba a makon da ya gabata ne, shugaban kasar Amerika Donald Trump ya bayyana gamsuwarsa da amincewarsa na mai da helkwatar Isra'ila zuwa birnin Qudus da kuma bayyana aniyarsa na dauke ofishin jakadancin Amerika daga Tel'abib zuwa birnin Qudus.

Nigeria

Nigeria

Nigeria

Nigeria

Nigeria

Nigeria

Nigeria